A lokacin da yake magana jiya a gaban kwamitin kula da harkokin siyasar wajen Amurka a majalisar dokokin kasar a Washington, jakadan tarayyar Najeriya a Amurka ya Adebayo Edifo ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya ba ta ji dadin yadda Amurka taki sayar mata da makamai ba, musamman ma ganin yadda kungiyar Boko Haram take ta kara karfi tare da mamaye birane a yankunan arewa maso gabacin kasar, ya ce yana fatan gwamnatin Amurka za ta sake yin nazari kan wannan batu.
Dangane da zargin da kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suke yi wa sojojin Najeriya da nuna bajinta wajen cin zarafin fararen hula a kasar kuwa, jakadan na Najeriya ya karyata wadannan rahotanni, inda ya ce sojojin Najeriya suna gunadar da aikinsu ne bisa ka'ida, kuma an san su da kiyaye dokoki da kiyaye rayuka da hakkokin farar hula. ABNA